Hikayata: Labarin Halitta Biyu

Hikayata: Labarin Halitta Biyu
An wallafa

A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo, yau mun kawo muku Labarin Halitta Biyu na Fai'za Abubakar da ke garin Gumel a jihar Jigawa- wanda Nabeela Mukhtar Uba ta karanta.

Labarin Halitta biyu labari ne da aka aka gina a kan wata matashiya da Allah ya jarrabe ta da lalurar halittar mata-maza.

Lamarin da ya sanya cikin tsangwama sakamakon kyama da hantara da ta fuskanta a wajen al'umma ciki har da mahaifinta.

Domin ta zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye, ta fuskanci tarin ƙalubalen ya kai har ga ta rasa mijin aure, duk a dalilin halittar da ba ita ta yi wa kanta ba.