'Matar da ta samar wa matasa fiye da 3000 aiki a Najeriya'

'Matar da ta samar wa matasa fiye da 3000 aiki a Najeriya'
An wallafa

Ambasada Fatima Mohammed Goni 'yar kasuwa da ke taimakon matasa wajen samar musu da ayyukan yi a fannoni daban-daban a Najeriya.

Ta kafa wata gidauniya da ake bai wa matasan dama su cike fom tare da saka takardun karatunsu da kofin katin zaɓe, a ajiye a ofishin gidauniyar, daga nan kuma sai ta yi ƙoƙarin nema musu aiki.

Ta ƙara da cewa tana samar wa matasan aikin, ba tare da la'akari da bambancin addini ba.

Ta ce ta samar wa matasa fiye da 3000 daga jihohi daban-daban na ƙasar aiki.