Ko uwa za ta iya dakatar da shayarwa na wani lokaci? 07/09/2024

Ko uwa za ta iya dakatar da shayarwa na wani lokaci? 07/09/2024
An wallafa

Iyaye mata masu shayarwa a wasu lokutan sukan tsinci kansu cikin wani yanayi ko wata lalurar da suke ganin ya kamata su dakatar da bai wa jariransu nono, amma da niyyar za su cigaba.

Sai dai likitoci ba sa bayar da goyon baya dakatar da shayarwar, ganin muhimmanci da ke tattare da shayar da nonon uwa ga jararai. ko da yake sun ce akwai wasu dalilai ƙalilan da a likitanci ke sa a cewa uwa ta dakatar da shayarwar.

Wasu bincike-binciken da aka yi a baya kan dakatar da shayarwa sun nuna cewa, ba duka iyaye matan da suka dakatar kan samu nasarar cigaba da shayarwar ba.

A cewar masana, shayar da nonon uwa abu ne dake da matuƙar muhimmanci, musamman ga jarirai a watanni shida na farko, lokacin da ya kamata su sha nonon zalla ba tare da an basu ruwa ba.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce nonon uwa na ƙunshe da abubuwan bayar da kuzari da dukkan sinadaran da jariri ke buƙata a watanni shida na farko a duniya.

Sannan ruwan nonon na bai wa jariri fiye da rabin abubuwan da jiki ke buƙata a yayin da ya haura wata shida zuwa shekara guda a duniya.

Haka zalika yaro kan samu kimanin kashi ɗaya bisa uku na abubuwan da ya ke buƙata a nonon uwa, bayan ya haura shekara ɗaya.

To domin jin irin dalilan da ke sanya wasu iyaye dakatar da shayarwa na wani lokaci da kuma abin da likitoci ke cewa kan wannan batu, latsa sautin da ke sama don samun cikakken shirin lafiya zinariya kan wannan batu.

Mun tattauna ne da kwararriyar likitar yara a Najeriya, Dr. Mariya Mukhtar Yola.