Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bishiyoyi bakwai da aka fi so a shuka a arewacin Najeriya
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
A yayin da duniya ke fuskantar barazanar dumamar yanayi, wadda ke yi wa halittun duniya barazana, masana na ci gaba da kiraye-kirayen shuka bishiyoyi a wani mataki na rage illar da ɗumamar yanayin ke yi wa duniya.
Dumamar yanayi fa faruwa sakamakon abubuwa da dama ciki har da kwararowar hamada, wadda ake samu sakamakon sare bishiyoyi da ake yi, lamarin da ke kusato da hadama ga mutane.
Kan haka ne masana da ƙungiyoyi da gwamnatoci a ƙasashe daban-daban ke gangamin kiraye-kirayen shuka bishiyoyi, domin dakile ƙaruwar illar dumamar yanayi da duniya ke fuskanta.
A shekarun baya-bayan nan duniya ta fuskanci zafin da ba a taɓa yin irinsa ba, lamarin da ya jefa al'umma cikin matsanancin damuwa sakamakon zafin ranar da suka fuskanta.
To sai dai baya ga magance matsalar ɗumamar yanayin masana na cewa akwai wasu nau'ikan bishiyoyi da suka fi amfani a cikin al'umma don haka ne ma suke son a mayar da hankali wajen shuka su saboda amfaninsu.
Dakta Dahiru Mahammd Hashim wanda ke shugabantar wani shiri na Bankin Duniya kan yadda za a takaita illolin sauyin yanayi a duniya, ya yi wa BBC ƙarin haske kan nau'ikan bishiyoyi bakwai da ya kamata a shuka, musamman a arewacin Najeriya, domin amfanin da suke da shi ga al'umma.
Masu sanyaya muhallai
Jami'in ya ce akwai nau'ikan bishiyoyin da ke taimakawa wajen sanyaya muhallin don amfanin ɗan'adam da dabbobi da tsuntsayen da ke rayuwa a kusa da su.
Dakta Dahiru ya ce irin waɗannan bishiyoyin jijiyarsu kan nutsa cikin ƙasa domin zuƙo ruwa mai yawa tare da riƙe shi, da kuma fitar da shi ta hanyar iska.
''Alal misali bishiyar turare masana sun ce tana iya zuƙo ruwa da ya kai lita 9,000, tare da fitar da ruwan ta hanyar iskar da suke fitarwa'', in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa''shi ya sa duk inda ka je ka samu bishiyoyin turare aƙalla biyu a wuri guda za ka ji wurin cike yake da sanyi''
''Binciken masana ya gano cewa sanyin da bishiyar turare ke fitarwa ya kai kwatankwacin sanyin da na'urar sanyaya ɗaki 10 za su fitar a lokaci guda'', in ji masanin muhallin.
Ire-iren bishiyoyin da ke sanyaya muhullai sun haa da bishiyar turare da ta malaina da mangoro da bishiyar zaitun da sauransu.
Masu fitar da iskar shaƙa mai kyau
Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya ce akwai kuma wasu nau'ikan bishiyoyin da ke samar da iskar shaƙa mai kyau domin taimaka wa lafiyar bil-adama.
Masanin ya ce irin wadannan bishiyoyi kan taimaka wajen gyara iskar da mutane ke shaka. Ya ci gaba da cewa ''wadannan bishiyoyi da za ka ga a koyaushe ganyensu na kaɗawa, saɓanin wasu da ke tsaye cak, to irin waɗannan bishiyoyi kan taimaka wajen gyara iskar da mutanen ke shaƙa''.
Masanin ya bayar da misali da bishiyar kanya, da darbejiya waɗanda ya ce koyaushe ganyensu na kaɗawa tare da fitar da iska mai sanyi da ke taimaka wa lafiyar numfashin ɗan'adam.
Masu samar da inuwa
Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya ce kowace bishiya na da wannan amfani na kare mutane daga zafin rana.
''Na daya daga cikin dalilan da muke kira ga mutane da su shuka bishiya shi ne tana taimaka wa wajen kare mutane daga zafin rana'', in ji shi.
Ya ce duk bishiyar da ke da ganye to zafin rana ba zai iya keta ganyen ba, don haka ganyen zai kare abin da ke kasan bishiyar daga zafin ranar da ake fuskanta.
Don haka ne masanan ki kiran a fifita shuka bishiyoyin da ke samar da inuwa sosai sabanin wadanda ba sa da wadatcciyar inuwa.
Misalan wadannan bishiyoyi sun hada da Tsamiya, da kanya da kadanya da gamji da baure da turare da sauransu
Masu samar da 'ya'yan itatuwa
Akwai bishiyoyin da ke samar da 'ya'yan masu amfani wajen kara wa mutane lafiya da kuma ba su kariya.
Masanin ya ce akwai nau'ikan bishiyoyi irinsu mangoro da kashu da lemo da gwanda sauran bishiyoyin ke da samar da 'ya'yan itatuwa.
''Haka kuma za ka samu irin waɗannan bishiyoyi ba iya mutane suke taimakawa ba, har da wasu nau'ikan tsuntsaye''.
Masu samar magunguna
Akwai bishiyoyin da ke taimaka wajen warkar da wasu nau'ikan cutuka tsakanin al'umma.
''Suma irin wadannan bishiyoyi muna kiran a yawaita shuka su saboda irin muhimmancin da suke da shi a cikin al'umma'', in ji shi masanin
Bishiyoyin da ke cikin wanann na'i sun hada da zogale da maɗaci da ararrabi da ɓaure da gamji da sauransu.
Masu ƙarfafa tattalin arziki
Suma wadannan bishiyoyi ne da ake yawan kiran shuka su saboda amfanin da suke da shi wajen kawo kudin shiga ga masu su.
Bishiyoyi ne da ake sayar da 'ya'yansu ko ganyensu somin samun biyan bukatu na rayuwa.
''Shuka irin wadannan bishiyoyi kan taimaka wa mai su wajen samun abin rufin asiri da biyan bukatunsa na yau da kullum'', in ji Dakta Dahiru Muhammad Hashim.
Ire-iren wadannan bishiyoyi sun haɗa da ɗorawa da dabino da kashu da mangoro da kaɗanya da sauransu.
Amfanin yau da kullum
Su kuma wadannan nau'ikan bishiyoyi ne da suke taimaka wajen gudanar da rayuwar yau da kullum.
Itatuwa ne da ake amfani da 'ya'yansu ko ganyensu domin yin mafnin yau da kullum, kamar abinci ko miya da kunu da sauransu.
''Suma wadannan nau'ika na itatuwa muna karfafa wa mutane gwiwwa da su shuka su ko don amfanin da suke da shi na yau da kullum'',in Dakta Dahiru Muhammad Hashim.
Misalan waɗannan bishiyoyi sun haɗa da kuka, da zogale da ake amfani da su wajen yin miya, sai tsamiya da ake amfani da ita wajen yin kunu.
A ina ya kamata a shuka bishiya?
Masani a harkokin kare muhallin ya ce, akan shuka bishiya ne a wurin da ba za ta fuskanci wata barazana ba.
''Yana da kyau duk inda za a shuka bishiya a lura cewa wuri da wata rana ba za a zo a ce ta haifar da matsala ba a wurin''.
Ya ci gaba da cewa ''ita bishiya idan za a shuka ta ba a son a shuka ta kusa da sokawe, ko kusa da katanga,saboda idan ta girma jijiyoyinta kan fasa katangar, lamarin da kuma ka iya haifar da faduwar gini ko gida baki daya''.
Haka kuma masanin ya ce ba a son shuka bishiya a kan hanya ko kasar wayoyin lantarki,saboda idan ta girma rassanta ka iya zama barazana wajen hada wayoyin wutar, wani abu da ka iya janyo gobara.
Bishiya na son a shuka ta a wuri mai kyau ko yake da fili ko yalwar wuri ta yadda za ta girma ta saki rassanta ba tare da wata matsala ba.
''Ita bishiya na son hasken rasa tare da iska, don haka idan aka shukata a inda za ta samu wadannan abubuwa to za ta girma tare da sakin rassanta yadda ya kamata ba tare da wata damuwa ba'', in ji masanin
Ya ya kamata a sare bishiya?
A wasu lokuta mutane kan sare bishiyarsu dungurumgum domin ta sake yin tofowa mai kyau.
To sai dai masanan na ganin cewa hakan bai dace ba, domin ba haka ya kamata a sare bishiya ba, suna masu cewa hakan na yin illa ga muhalli.
''Babu wani dalili da zai a sare bishiya,dungurungum, sai dai a rageta idan wani dalili ya kama, to anan in dalilin ya kama ba a so a asketa gaba daya, abin da ya kamata shi ne sai a sare reshen da ya haifar da matsalar'', in ji.
Ya ce dalilan da ke sanya a aske bishiya su ne kamar a ce wani reshe nata ya kwanta a kan rufin daki ko kan hanya.
Wani dalilin da ke sa mutane su sare bishiya shi ne don neman makamashin da za su kona wajen girka, to sai masanin ya ce a nan in hakan ya kama, abin da ya kamata a yi shi ne a sari reshe daya a bishiya daya, sai a tafi wata bishiyar ita ma a sari guda daya a haka ahr a samu abin da ake bukata.
''Gaskiya babu dalilin da zai sa sare bishiya dungurungum'', in ji shi.
Inuwar bishiya na hana amfanin gona?
Wani dalilin da ya sa wasu mutanen ke sare bishiyoyi a gonakinsu shi ne domin samun amfanin gona mai karfi, kasancewa idan aka yi shuka a karkashin bishiya rashin hasken rana kan sa a wasu lokutan amfanin ya gaza, ko ya ki yi ma gaba-daya.
Anan masana na ganin cewa abin da ya kamata shi ne masu gona su shuka amfanin da yake yi a inuwa.
''Akwai nau'ikan amfanin da ake shukawa da su inuwa ba ta hana su yi, ko ma mu ce sun fi son inuwar, don haka muna kira ga manoma da su rika shuka irin wadanann nau'ikan amfani maimakon sare bishiyoyi'', in ji masanin.
Ya ci gaba da cewa amfanin da bishiyar za ta yi maka, bai kai amfanin da abin da ka shukan zai yi maka ba.
Akwai dai nau'ikan amfanin da ake shukawa kuma su yi kyau a inuwa, kamar kubewa da borkono da tumatir da yakuwa da wata nau'in dawa da ake kira zauna-inuwa.