Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya ta gargaɗi Netflix kan fina-finan da ke keta dokokin Musulunci
Ƙasashen Larabawa na yankin Gulf sun nemi kamfanin Netflix ya cire dukkan fina-finan da suka saɓawa dokokin Musulunci da al'adun tabiyya, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Saudiyya ta ruwaito.
A wata sanarwa da ƙungiyar ƙasashen yankin Gulf ɗin ta fitar ta yi gargadi cewar wasu fina-finai na baya-bayan nan da aka yi don yara sun saɓa wa dokoki.
Sai dai ba a yi wani ƙarin bayani ba. Amma kafar talabijin ta Saudiyya ta nuna wasu bidiyo da aka dusaseh fuskarsu na katun ɗin fim ɗin Jurassic World: Camp Cretaceous, wanda aka nuna wasu yara mata biyu suka nuna suna son juna tare da sumbatar juna.
Gidan talabijin na Al Ekhbariya da ya nuna wani sashe na fim ɗin da wani kamfanin Faransa na Cuties ya shirya, ya sanya take kamar haka "bidiyon da ke nuna rashin ɗa'a da rusa tarbiyya wanda ke barazanar lalata tarbiyyar yara."
A wani bidiyon da Al Ekhbariya ta wallafa a shafinta na intanet ta yi zargin cewa fim ɗin na "yaɗa luwaɗi da maɗigo ne."
Kazalika gidan talabijin ɗin ya yi hira da mutane da dama da suka yi irin wanan zargin tare da kiran hukumomi su ɗauki mataki cikin gaggawa.
An tuntuɓi Netflix da ya cire bidiyon, da kuma duk wasu fina-finai da aka shirya don yara, tare da tabbatar da bin dokoki," kamar yadda sanarwar haɗin gwiwa daga hukumar kula da fina-finai ta Saudiyya da ta kula da kafafen yaɗa labarai.
Hukumomi za su sa ido don ganin ko an bi umarnin, tare da ɗaukar matakan shari'a idan har aka ci gaba da yaɗa fina-finan", kamar yadda suka yi gargaɗi.
Babu wani martani daga kamfanin Netflix. Duk da cewa Saudiyya ba ta da wasu dokoki na damar zaɓar jinsi, amma yin luwadi da madigo da zina haramun ne a ƙasar.
A ƙarƙashin dokokin Musulunci na ƙasar dai, hukuncin duk wanda aka kama da laifin luwaɗi ko madigo hukuncinsa shi ne kisa ko bulala, ya dangata girman laifin.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
A watan Afrilu, sinimomi a Saudiyya ba su nuna wani fim mai taken 'Doctor Strange' ba bayan da hukumomin ƙasar suka ce akwai abubuwan da suka shafi luwaɗi da maɗigo a cikinsa.
Sannan a watan Yuni ma an haramta kallon wani fim na katun da ke yaɗa aƙidar auren jinsi a Saudiyyan da kuma ƙasar haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
A watan da ya gabata kuma hukumomin Saudiyya sun zargi Youtube da sanya wasu tallace-tallace na keta dokokin Musulunci.