Lafiya Zinariya: Yara mata 'sun fi maza daina fitsarin kwance'

Lafiya Zinariya: Yara mata 'sun fi maza daina fitsarin kwance'
An wallafa

Fitsarin kwance matsala ce da ta zama ruwan-dare a tsakanin yara, sai dai idan sun haura shekara goma, mazan da ke ci gaba da fitsarin sun fi mata yawa.

Likitoci sun alakanta hakan da yanayi na halitta. Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce fitsarin kwance abu ne marar dadi, amma yara da dama suna dainawa a kashin kansu.

Shawarwarin da ta bai wa iyaye kan abin da za su iya yi a gida don taimaka wa 'ya'yansu su daina fitsarin na kwance su ne: a bai wa yaro ruwa isasshe ya sha da rana, kuma ya dinga yawan zuwa fitsari.

Sannan ya yi fitsari idan zai kwanta bacci. Iyaye za kuma su iya sanya leda a kan shimfidar yaro sannan su tabbatar yaro zai iya zuwa bandaki a cikin sauki da dare.

Sai dai hukumar ta ce iyaye kada su bai wa yaro horo saboda ya yi fitsari a kwance don ba laifinsu ba ne, yin hakan zai iya dagula lamarin.

Sannan kada a bai wa yaran abin sha da ke dauke da sinadrin kofi (cafaine) kamar ganyen shayi da gahwa da cola, domin za su kara sanya su yin fitsarin.

Wani abin da kuma hukumar ta ce iyaye su daina yawan yi shi ne, kai yara fitsari da dare, domin hakan ba zai taimaka wa yaro ba.

Amma idan duk hakan bai yi aiki ba sai a je asibiti, domin sanin ko akwai bukatar magani.