Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Kan zargin Tinubu da fifita Yarabawa a rabon muƙamai
A Najeriya, jama'ar ƙasar na ci gaba da tsokaci a kan naɗe-naɗen manyan jami'ai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi, waɗanda wasu ke zargin yana fifita ƙabilarsa ta Yarabawa.
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijan Najeriya, na daga cikin masu wannan zargi, yana mai cewa abin da shugaban ƙasar ke yi ya saɓa wa tsarin mulkin ƙasar, wanda Shugaba Tinubu ya rantse da Alƙur'ani zai kare.
Sai dai fadar shugaban Najeriya ta ce zargin da ake yi wa Bola Tinubu na fifita ƙabilarsa wajen naɗe-naɗen muƙamai, ba gaskiya ba ne.
A filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, mun tattauna da Sanata Ali Ndume ko me ya sanya shi yin wannan zargi?