Lafiya Zinariya: Kan illar shaye-shaye tsakanin mata

Lafiya Zinariya: Kan illar shaye-shaye tsakanin mata
An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tabar wiwi ce ƙwayar da aka fi ta'ammali da ita tsakanin miyagun ƙwayoyi a duniya.

WHO ta ce kimanin mutum miliyan 129 zuwa 190 ne ke ta'ammali da tabar wiwi a faɗin duniya.

A cikin shirin namu na wannan makon Habiba Adamu ta duba shaye-shayen ƙwayar tsakanin mata, da kuma irin illar da shaye-shayen ke yi wa mata.