Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Forest ta ci gaba da zama ta ukun teburin Premier
Nottingham Forest ta ci Manchester City 1-0 ta hannun Callum Hudson-Odoi a wasan mako na 28 a Premier League ranar Asabar a City Ground.
Wannan nasarar ta sa Forest na ci gaba da fatan samun gurbin Champions League a gasar baɗi.
Odoi mai shekara 24 ya ci ƙwallon ne, bayan da Morgan Gibbs-White ya ba shi tamaula, shi kuma ya zura a ragar Ederson, saura minti bakwai a tashi karawar.
Ba a samu damar maki da yawa ba a karawar, sai dai kaɗan ya rage City ta zura ƙwallo a raga ta hannun Nico Gonzalez tun kan hutu.
Bayan sun yi hutu sun koma zagaye na biyu, Hudson-Odoi ya buga ƙwallo, amma Ederson ya taɓa ta je ta bugi turke.
Wasan farko da Forest ta yi nasara a kan City a lik tun bayan 1997.
Da wannan sakamakon Forest ta ci gaba da zama a mataki na ukun teburi da maki 51, saura wasa 10 a ƙare kakar bana.
City mai rike da Premier ta ci gaba da zama ta huɗun teburi da maki 47, watakila Chelsea ta karɓe gurbin mai maki 46 da zarar ta doke Leicester ranar Lahadi.