Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaratan mata masu tsaro a wajen taruka da ake zaton 'ƴan maɗigo ne'
Kun taɓa ganin tawagar masu tsaron wuraren taruka ta mata zalla?
Wannan ce tawagar da Emem Thomas ke jagoranta, ta mata zalla masu tsaro a wuraren taruka ko tsaron wasu manyan mutane a Najeriya.
Thomas a yayin da take hira da BBC Pidgin ta ce mutane na musu dariya ita da tawagarta saboda su mata ne.
"Mutane dariya suke mana sosai har da faɗuwa wani sa'in, suna zolayarmu da cewa ko dai zani muke ɗaurawa mu yi ta rawa a bukukuwan mutane".
Ana mana kallon ƴan maɗigo
Thomas ta ce mutane ba su dauke su da muhimmanci ba, wasu ma har tunani suke ko mu ƴan madigo ne.
Amma abin da mutane ba su sani ba shi ne tawagata ta musamman ce.
Ta ƙara da cewa wani lokacin mutane na musu kallon ƙasƙanci saboda su mata ne.
"Ƴan Najeriya ba su yarda cewa mata za su iya wannan aikin ba. Suna tunanin kawai idan muka tsaya yanga muke yi.
"Abin da ya sa tawagata ta zama ta musamman shi ne saboda ina zaɓo mata masu ƙiba, masu kyau, jajirtattu, kuma waɗanda suka iya aikin.
Matar ta ce mazan da ta gani suna irin wannan aikin ne ya sa ta fara samo mata masu ƙaƙƙarfan jiki saboda su yi aikin.
Ta ce abu mafi muhimmanci a zaɓen matan shi ne sai mai ingarman jiki.
Thomas ta ce ita ma ta yi aikin nan bayan da ta kammala karatu saboda rashin aikin yi.
"Lokacin ne na bayar da shawarar mu samo masu tsaro, sai kuma daga baya suka ce ba sa son mata. Muka yi ta muhawara akai, daga baya na ce bari kawai in yi abuna ni kadai.
"Sai na fara a shekara ta 2018. Emem Thomas ta ce tana da dabarun da take bi daban-daban a tarurruka saboda kar a raina aikin mata ne.
Ta ce yayin da wasu ke ƙasƙanta su, suna birge wasu mazan.
Thomas ta ce ba ta tunanin za ta saka maza a cikin ma'aikatanta, abun da kawai muke yi shi ne bayar da horo, kuma matan da nake dauka duk halittar jikinsu ce irin ta waɗanda za su iya aikin ne.