Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rigar da ke taimaka wa masu larurar shanyewar jiki su yi tafiya
Rigar da ke taimaka wa masu larurar shanyewar jiki su yi tafiya
An wallafa
Mutanen da ke fama da larurorin da ke da alaka da kwakwalwa irin su shanyewar jiki sukan sha wahala wajen yin motsi.
Sai dai yanzu an kirkiro wata sabuwar riga da ke taimaka musu wajen rage jin radadi da kuma samun damar yin tafiya. Rigar mai suna Exopulse Mollii tana aike wa da wasu sakonnin lantarki da suke tausasa jijiyoyi. Hakan babban abin karfafa gwiwa ne ga mutanen da ke fama da wannan larura.