Mutum 6 da ke kan gaba a neman shugabancin Majalisar Dinkin Duniya

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da wa'adin mulkin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), António Guterres, ke zuwa ƙarshe a watan Disamban 2026, hankalin duniya ya fara karkata zuwa ga fafatawar neman wanda zai gaje shi.

Takarar muƙami, wanda ake kallo a matsayin ɗaya daga cikin mafi muhimmanci a harkokin diflomasiyyar duniya, na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fama da yaƙe-yaƙe, rikice-rikicen siyasa da matsalolin tattalin arziki da sauyin yanayi.

A wannan karon, akwai ƴan takara daga yankuna daban-daban na duniya da suka fito domin neman shugabancin wannan babbar cibiya ta duniya.

Wasu daga cikinsu tsoffin shugabannin ƙasashe ne, yayin da wasu kuma suka shafe shekaru suna riƙe da manyan mukamai a cikin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran cibiyoyin duniya.

Kodayake har yanzu babu tabbacin wanda zai yi nasara, akwai sunayen da ke ci gaba da fitowa a rahotanni da tattaunawar masu bibiyar harkokin MDD a matsayin waɗanda ke kan gaba wajen neman kujerar.

Rebeca Grynspan (Costa Rica)

Rebeca Grynspan ita ce shugabar Hukumar Kasuwanci da Raya Tattalin Arziki ta MDD (UNCTAD) a yanzu hana.

Ta kasance tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasar Costa Rica da ke yankin Latin Amurka.

Ms Grynspan ta shafe shekaru tana riƙe da manyan muƙamai a Majalisar Dinkin Duniy.

Masu goyon bayanta na ganin gogewarta a fannin ci gaba da tattalin arziki zai taimaka mata wajen jagorantar majalisar a lokacin da ake fama da matsalolin tattalin arzikin duniya.

Rafael Grossi (Argentina)

Rafael Grossi shi ne Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

Ƙwararren masanin diplomasiyyar makamshi ne, wanda ya yi suna wajen shiga tsakani a batutuwan nukiliya masu sarƙaƙiya, musamman a rikice-rikicen da suka shafi Iran da Ukraine.

Mista Grossi ya kasance tsohon jakadan Argentina a ƙasashen Austria da Belgium da Luxembourg, sannan ya riƙe muƙamin mataimakin daraktan hukumar IAEA kafin aga baya ya zama shugabanta a 2019.

Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'yan takarar saboda ƙwarewarsa a harkokin diflomasiyya da tsaro na duniya.

Michelle Bachelet (Chile)

Tsohuwar shugabar ƙasar Chile, Michelle Bachelet, na daga cikin fitatun yantakarar shugaban Majalisar Dinkin Duniyar.

Ms Bachelet ta riƙe muƙamin Babbar Kwamishinar Kare Haƙƙin Dan Adam ta MDD.

Ta kasance ɗaya daga cikin fitattun mata masu tasiri a siyasar duniya.

Idan aka zaɓe ta, za ta zama mace ta farko da ta jagoranci Majalisar Ɗinkin Duniya a tarihinta

Macky Sall (Senegal)

Tsohon shugaban ƙasar Senegal da ke Yammacin Afirka, Macky Sall ya shiga takarar ne da goyon bayan wasu ƙasashen Afirka.

Sall na jaddada muhimmancin zaman lafiya da girmama ikon ƙasashe.

Masu sa ido na ganin Afirka na da hujjar neman wannan kujera saboda nahiyar ba ta cika samun wannan dama sosai ba.

Tun bayan kafa Majalisar Dinkin Duniya ƴan Afirka biyu ne kawai suka taɓa jagorantarta, Boutros Boutros-Ghali ɗan asalin Masar (1992–1996) da Mista Kofi Annan daga Ghana (1997–2006).

María Fernanda Espinosa (Ecuador)

María Fernanda Espinosa ta taɓa zama shugabar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Ms Espinosa ta kasance tsohuwar ministar harkokin wajen ƙasar Ecuador da ke kuancin Amurka.

Tana daga cikin ƴan takarar da suka fi mayar da hankali kan gyaran tsarin MDD da ƙarfafa haɗin kan ƙasashe wajen tunkarar matsalolin duniya.

Carolyn Rodrigues Birkett (Guyana)

Carolyn Rodrigues Birkett na cikin jerin masu burin zaman shugaban MDD na gaba.

A halin yanzu ita ce jakadiyar Guyana a Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma tana da gogewa mai yawa a harkokin gwamnati da diflomasiyya.

A baya ta riƙe muƙaman minista da dama a ƙasarta, ciki har da ma'aikatar cikin gida da ma'aikatar albarkatun ƙasa.

Masu goyon bayanta na bayyana ta a matsayin ƴar takarar da ke da gogewa a fannoni biyu masu muhimmanci, wato shugabanci a matakin ƙasa da kuma aiki a tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Haka kuma kasancewarta daga yankin Caribbean na iya ƙara mata armashi, ganin cewa ba a taɓa samun Sakatare Janar daga wannan yanki ba.

Me ya sa matsayin ke da muhimmanci?

Masu sa ido kan harkokin MDD na ganin zaɓen wanda zai gaji Guterres ba zai kasance mai sauƙi ba, duba da yadda manyan ƙasashe masu kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro ke taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai kai ga matakin ƙarshe.

Haka kuma, batun wakilcin yankuna da kuma kiran da ake yi na bai wa mata damar shugabantar MDD a karon farko na daga cikin muhimman abubuwan da za su iya tasiri a zaɓen.

Akwai masu fafutikar ganin an zaɓi mace a karon farko cikin shekaru 80 na tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sabon Sakataren MDD zai karɓi ragamar shugabancin majalisar ne a lokacin da duniya ke fama da yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen siyasa da sauyin yanayi da matsalolin tattalin arziki.