Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin mene ne ke janyo warin balaga?
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa akwai wasu kwayoyin cuta wadanda sukan sa mutum ya yi warin jiki tamkar wani rubabben kifi.
Haka kuma wasu cututtuka kamar ciwon hanta da ciwon suga idan suka yi tsanani su ma sukan janyo mutum ya dinga wari kamar warin kifi.
Yawancin warin da aka fi sani shi ne warin da matasa ke yi idan suka kawo shekarun balaga, wanda aka fi sani da warin balaga.
Mata masu jiki su ma su kan samu warin jiki.
Sai dai a jikin mutane akwai wasu wurare da kan yi wari wadanda suka hada da baki da hammata da kuma al'aura.
Ko da yake likitoci sun bayyana cewa tsaftace wadannan wurare ta hanyar wanke su da kuma cire gashin da ke nan na taimakawa wajen kawar da warin da ake samu.
Wasu masu wannan matsala dai musamman a tsakanin matasa su kan fuskanci tsangwama a tsakanin tsararrakinsu ko a cikin al'umma.