An yi wa gidan talabijin ɗin Iran kutse ana tsaka da labarai

An wallafa

An yi kutse ga labaran da ake gabatarwa na talabijin kai tsaye a gidan talabijin ɗin ƙasar Iran.

An yi kutsen ne da niyyar zanga-zanga ga jagoran ƙasar. A daidai lokacin da ake gabatar da labaran, kawai sai aka ga hoton fuska wadda aka rufe ta fito a gaban talabijin, sai kuma hoton jagoran addini na ƙasar Ali Khamenei da kuma wuta tana ci a bayansa.

Waɗanda suka yi kutsen na kiran kansu da "Adalat Ali" wato Adalcin Ali.

Wannan na zuwa ne aƙalla kwana uku bayan an harbe aƙalla mutum uku a cikin masu zanga-zangar a lokacin da suka yi arangama da jami'an tsaro a wani sabon rikici kan rasuwar Mahsa Amini.

Ms Amini dai ta kasance wata mata wadda ƴan sandan Hisbah na Iran suka kama ta saboda zargin ƙin rufe kanta yadda ya kamata.

Kama ta da aka yi ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a ƙasar inda aka yi ta gudanar da zanga-zanga.

Labaran ƙarfe shida na yamma ne dai aka yi wa kutsen inda bayan nuno hoton jagoran addini a ƙasar sai kuma aka nuno hotunan Ms Amini da wasu mata uku waɗanda aka kashe su a yayin zanga-zanga ta baya-bayan nan da ake yi.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka rubuta a jikin talabijin ɗin a yayin kuten shi ne "ku tashi ku bi mu," inda wani rubutun kuma ke cewa "matasanmu, jini na zuba daga hannunku".

Wannan kutsen an yi shi ne na ƴan daƙiƙoƙi kafin aka katse labaran. Irin waɗannan zanga-zangar da ake yi ga jagoran addinin ba a saba ganinsu ba inda yake da ƙarfi matuƙa a Iran.

Sai dai bayan rasuwar Ms Amini, sai aka soma fitowa ƙiriƙiri ana ƙalubalantar sa.

Haka kuma ko a ranar Asabar sai da wasu bidiyoyi na kafofin sada zumunta suka rinƙa yawo inda aka rinƙa ganin wasu mata ƴan jam'ia suna ihun "ka ɓace" a lokacin wata ziyara da Shugaba Ebrahim Raisi ya kai.

Haka kuma a ranar ma sai da aka kashe mutum biyu a Sanandaj, ciki har da wani mutum da aka harba a cikin motarsa bayan ya matsa odar motarsa domin goyon bayan zanga-zangar.

Haka kuma wani bidiyo ya nuna yadda aka harbi wata mata a wuya inda aka ganta kwance a ƙasa.

Rasuwar Ms Amini dai ita ta jawo duk waɗannan rikice-rikicen duk da cewa gwamnatin ƙasar ta tabbatar da cewa rashin lafiya ce ta yi sanadin mutuwarta ba wai azabtarwa ba.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun ce sama da mutum 185 ne aka kashe tun bayan da aka soma irin wannan zanga-zanga a Iran a ranar 17 ga watan Satumba.