Peljto ne zai busa wasan Arsenal da Real a Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Turai ta bayyana Irfan Peljto a matakin wanda zai yi alkalancin wasan Arsenal da Real Madrid a Champions League.

Ranar Talata filin wasa na Emirates zai karɓi bakuncin wasan farko a kwata fainal a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai tsakanin Gunners da Real Madrid.

Wannan shi ne karo na biyu da ɗan kasar Bosnia zai busa wasan da ya shafi Real Madrid a Champions League.

Wasan da Peljto ya yi alkalanci a karawa da Real Madrid a Champions League:

1. Leipzig 0-1 Real Madrid. wasan farko zagayen ƴan 16 a kakar 2023/24.

Real Madrid ta kawo matakin nan, bayan da ta fitar da Atletico a bugun fenariti da cin 4-2.

Ita kuwa Arsenal ta yi waje da PSV Eindhoven da cin 9-3 gida da waje a wasannin bana.

Real Madrid mai rike da Champions League tana da 15 jimilla, yayin da Arsenal ke fatan lashe na farko a tarihi.

Real Madrid tana ta biyun teburi a La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama, bayan kammala wasan mako na 30.

Itama Gunners tana ta biyu a teburin Premier League, amma da tazarar maki 11 tsakani da Liverpool, mai fatan lashe kofin bana kuma na 20 jimilla.