Gane Mani Hanya: Muna da burin haɗa kan ƙungiyar Ecowas – Barau Jibrin

Gane Mani Hanya: Muna da burin haɗa kan ƙungiyar Ecowas – Barau Jibrin
An wallafa

Sabuwar majalisar dokokin Ecowas zango na shida da aka ƙaddamar a baya-bayan nan, ta ce za mayar da hankali wajen ganin ta inganta haɗin kai da ƙarfafa zumunci tsakanin ƙasashen yankin Afirka ta Yamma.

A ranar 6 ga watan Afrilun nan ne, aka ƙaddamar da sabuwar majalisar a Abuja, babban birnin Nijeriya, daidai lokacin da Ecowas ke fuskantar babban ƙalubale na barazanar ɓallewar wasu ƙasashe mambobinta.

Sabon shugabancin majalisar dokokin na Ecowas, ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ƙasashen, sun koma kan turbar dimokraɗiyya.

Kan haka Buhari Muhammad Fagge ya tattauna da Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattijai ta Najeriya, kuma mataimakin shugaban majalisar Ecowas na 1, kuma mai riƙon muƙamin kakaki, ya zuwa lokacin da za a zaɓi tabbataccen shugaba daga ƙasar Togo.