'Ɗana ya fi sanin ƙarar bama-bamai a kan ƙarar kayan wasansa'

    • Marubuci, Lara El Gibaly and Haya Al Badarneh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Cikin 'yan kwanaki da fara kai hare-haren Isra'ila a Gaza a Oktoban bara, Falasɗinawa biyu suka fara naɗar wa BBC rayuwarsu ta yau da gobe. Aseel ya tsere zuwa kudancin zirin na Gaza domin neman tsira, Khalid kuma ya zaɓi ya ci gaba da zama a arewacin yankin. Tsakaninsu, sun yi ta adana labaran bama-bamai da tserewar mutane da mace-mace da kuma ɗimuwar da yara ke fuskanta sakamakon rikicin.

Khalid

Zaune a ƙasan wani ɗaki da bam ya yi wa fata-fata a arewacin Gaza, Hamoud ne ɗan shekara shida da Halloum mai shekara huɗu, suna wasan ba da agaji. Sun saka wata ƴartsana a tsakaninsu inda suka ɗora bandejin wasa a cikin kayan ƴarbebin.

"Ta ji ciwo," in ji Hamoud. "Ɓuraguzai da dama sun faɗa kanta."

Yanayi ne da shi da ɗanuwansa suka sha gani yana faruwa cikin shekarar da ta gabata a Gaza, inda kusan ɗaya cikin mutum uku da ake kashewa a yaƙin da ya soma a Oktoban 2023, yaro ne, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana.

An ƙaddamar da yaƙin Isra'ila bayan kashe kusan mutum 1,200 a hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Khalid, mahaifin yaron na kallonsu cikin yanayi na marari daga nesa yayin da suke wasa.

"Ba wasanni bane da ya kamata a ce yara su yinsa ba," in ji Khalid. "Idan na gansu haka, zuciyata tana rauni."

Yayin da asibitoci a arewacin Gaza suka daina aiki a Disamba, ƴan watanni bayan soma yaƙin, Khalid ya bijirewa umarnin Isra'ila na ficewa daga kudanci inda ya yanke shawarar ci gaba da zama a Jabalia da ke arewacin Gaza domin samar da magunguna ga al'ummarsa.

Khalid ba likita bane, amma ya samu horo a matsayin mai bai wa gaɓoɓin jiki da suka samu illa kulawa sannan ya taɓa aiki a matsayin mai rarraba magunguna.

"Kowa a yankinmu ya san ni mai kula da gaɓoɓin jiki ne idan suka samu illa, ba likita ba. Amma da aka shiga wannan yanayi, na faɗa masu cewa zan iya sauya bandeji na kuma yi ɗinki idan aka ji rauni musamman ga yara. Idan na tafi, waɗanda nake kula da su za su iya rasa rayukansu saboda babu asibitoci."

Kasancewar akwai rashin kayan aikin tiyata da kuma cikar wa'adin aikin wasu magungunan, ya sa Khalid ya buɗe cibiyar kula da lafiya a gidansa, inda ya mayar da hankali wajen kula da yara. Sai ƴaƴansa suka soma kwaikwayon abin da suke gani.

"Motar ɗaukan mara lafiya, kai shi cikin motar ɗaukan mara lafiya! Hamoud ya faɗa cikin ɗaga murya yayin da shi da ƴaruwarsa suke wasan jami'an lafiya,' ɗaya daga cikin sabbin wasannin da suka ƙirƙira yayin yaƙin. Khalid na iya jiyo muryar ɗansa yana ƙoƙarin gano yanayin raunin. Ko rauni ne na harin makami mai linzami ko kuma sakamakon rushewar gini?

"Hamoud ya fi sanin ƙarar bama-bamai a kan ƙarar kayan wasan shi. Sannan dole ta sa Halloum jurewa yanayin da ta tsinci kanta ciki duk da ƙarancin shekarunta," in ji Khalid. "Ina tsoron irin tasirin da yaƙin zai yi ga ƙwaƙwalwarsu."

Ƙungiyar agaji ta ICRC ta ce tasirin ɗai-ɗaita da ɗimuwa da rashin zuwa makaranta a kai a kai suna da tasiri sosai kan yara a Gaza.

Ba iya ɗimuwa kaɗai ƴaƴan Khalid ke fuskanta ba kasancewar sun maƙale a arewacin zirin, har da yanayi na yunwa da ba a taɓa gani ba. A Yuni, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa kashi 96 cikin 100 na mutanen Gaza na fama da matsananciyar matsalar abinci.

Yayin da Hamoud ke ɗaga tuta a saman rufi, da ke alamta wa wani jirgin agaji buƙatar ya jefo ƙunshin kaya kusa da gidansu, wata ƙara mai firgitarwa ke girgiza ƙasa. Yanzu wani jirgin Isra'ila ya jefa bam kan wani gini da ke kusa, wani baƙin hayaƙi ake iya gani daga kusa da gidansu.

"Ba na son jiragen da ke jefo bama-bamai," in ji Hamoud. "Ina son su riƙa jefo mana abinci."

Aseel

A kudancin Gaza, Aseel, mai shekara 24 wadda ta haihu a baya-bayan nan na duba yadda za ta shayar da ƴarta Hayat.

"Babu abinci a kasuwa da zan iya ci har ma na shayar da ita, dole sai na haɗa da madara," in ji Aseel.

Hukumar kula da yawan al'umma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) ta yi gargaɗi a wannan watan cewa masu juna biyu 17,000 a Gaza suna gab da faɗa wa ƙangin yunwa.

"Madarar gwangwani, ƙunzugun yara da duk wani abu da jarirai ke buƙata sun ƙara tsada yayin yaƙin," in ji maigidan Aseel, Ibrahim. Samun su ma wani aiki ne, in ji shi.

Ba haka Aseel ta yi hasashen renon ƴarta zai kasance ba.

Aseel da mijinta da kuma ƴarsu ƴar wata 14, Rose sun tsere daga gidansu inda suka tunkara kudancin zirin a makonnin farko na yaƙin, inda suka bi shawarar Isra'ila na mutane su fice daga yankin. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa Falasdinawa tara cikin 10 a Gaza sun rasa muhallansu aƙalla sau ɗaya tun soma yaƙin a Oktoban 2023.

A lokacin tana da juna biyu na wata takwas amma dole ta sa ta yi tattaki mai tsawo zuwa kudancin Gaza ta wata hanya da aka bayyana tana da tsaro. "Ba mu samu isasshen ruwa ba kuma ina fama da ƙarancin jini. Akwai gawawwaki birjik a ƙasa. Abin da kawai nake tunani shi ne ɗiyata Rose da kuma jaririn da ke cikina."

Aseel da mijinta sun yi wata yarjejeniya, ta ce "idan wani wani abu ya faru da shi, zan ci gaba da tafiya ni kaɗai sannan na ɗauki ɗawainiyar kula da ƴarmu Rose da jaririyar. Sannan idan na suma saboda gajiya, ya san kawai zai ci gaba da tafiya ne da ƴarmu ya bar ni a baya."

Da zarar sun isa inda ake da tsaro a Deir al-Balah da ke kudanci, wata matsalar ta ɓullo: babu asibitoci da ke aiki idan za ta iya haihuwa. Asibitin Al Awda a Nuseirat ne kaɗai asibitin da ke kusa da ke iya karɓar haihuwa.

An haifi ƴar Aseel, Hayat a can ranar 13 ga watan Disamba. Sunanta na Larabci da ke nufin rayuwa, an zaɓe shi ne a matsayin wani tuni ga rayuwar jin daɗi da farinciki da suke fatan koma wa da zarar an daina yaƙi.

"Kamar ta dawo da rayuwata ne, ana tsaka da wannan ɓarna. Tana tuna min cewa za a iya ci gaba da rayuwa ko da cikin yanayi mafi ƙalubale."

Ibrahim mai ɗaukar hoto, ya tafi ya bar matarsa da ƴarsa Rose da kuma jaririyarsu a baya domin ya je ya ɗauki hotuna abin da ke ƙara jefa shi cikin haɗari na tallafa masu.

Bayan da wani abu ya faru da ya samu kansa cikin tsaka mai wuya, ya ce "Ina yin duka waɗannan domin biyan buƙatunsu na yau da kullum, ƙunzugun yara da madarar gwangwani da kuma kayan saw."

"Ina ji kamar nauyin Gaza baki ɗaya na kan kafaɗata. Na damu sosai da ƴaƴana kuma ina jin kamar bana iya biyan buƙatun jaririyata."

A Mayu, Ibrahim da Aseel sun sake haɗuwa a Deir al-Balah inda suka je wajen shaƙatawa da yaransu.

"Hayat ba ta san wata rana da ba a yaƙi ba," in ji Ibrahim. "An haife ta ana tsaka da yin ɓarna, ana tsaka da jin ƙararrakin fashewar bama bamai da kuma labarai marasa daɗin ji."

Hayar ƴar wata shida na kan cinyar mahaifiyarta a gaban mota. Motar na tafiya ne ta kan wasu rusassun gine-gine da suka bazu kan titunan da ƙasa da tarkace suka mamaye.

"Sai dai duk da waɗannan," in ji Ibrahim, "tana ci gaba da murmushi."