Kano Pillars ta fara Premier ta bana da kafar dama a Katsina

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kano Pillars ta yi nasarar doke Ikorodu United 3-0 ranar Lahadi a wasan makon farko da fara gasar Premier ta Najeriya ta 2024/25.

Pillars ta buga wasan ne a jihar Katsina, bayan da ake gyaran filin wasanta na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Najeriya.

Pillars ta ci ƙwallayen ta hannun Mustapha Umar da Rabiu Ali da ya zura biyu a raga, mai shekara 43 yana buga kaka ta 18 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.

Da wannan sakamakon Pillars, wadda ake kira sai masu gida tana ta ɗaya a kan teburi da maki uku, sai Sunshine Stars ta biyu da maki uku.

Enyimba ce ta uku da maki uku, sauran da suke da maki uku a karawar makon farkon sun haɗa da Remo Stars da Niger Tornadoes da Plateau United.

Wannan kakar ce ake kokarin ɗora jadawalin wasannin Premier na Najeriya, domin a kammala gasar lokaci ɗaya da na sauran kasashen duniya.

Hakan zai bai wa ƙungiyoyin damar shirin shiga gasar zakarun Turai da sauran manyan wasanni a kan kari da samun hutun ƴan kwallo iri ɗaya da na sauran gasar duniya.

Sakamakon wasannin makon farko

Ranar Lahadi 8 ga watan Satumba

  • Abia Warriors 0-2 Remo Stars
  • Sunshine Stars 3-0 Bayelsa Utd
  • Nasarawa Utd 1-1 3SC
  • Heartland 1-3 Enyimba
  • Kwara Utd 1-2 Tornadoes
  • Bendel Insurance 0-0 Rivers Utd
  • Kano Pillars 3-0 Ikorodu City
  • Plateau Utd 1-0 Katsina Utd

Za a buga wasa ɗaya ranar Litinin tsakanin Lobi Stars da Akwa United

Ranar Asabar 31 ga watan Agusta

  • Rangers 0-0 El Kanemi Warriors