Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Tare da Attahiru Bafarawa
Gane Mini Hanya: Tare da Attahiru Bafarawa
An wallafa
A wannan mako ne, wasu jiga-jigan ƴan siyasa a arewacin Nijeriya suka ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya ko tafiya mai suna Northern Star Empowerment Initiative, a yunƙurinsu na haɗa kan al'ummar yankin da zaburas da matasa.
Sun ce sabon yunƙurin na da alaƙa da tsamo arewacin Nijeriya daga matsalolin da yake fama da su, kamar na taɓarɓarewar tsaro da rashin aikin yi da ƙaruwar fatara, baya ga ƙarancin abinci da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Jagoran ƙungiyar, Alhaji Ɗalhatu Attahiru Bafarawa kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto ya ce lokaci ya yi da za su jagoranci matasa su karɓi ragama.