Chelsea na shirin miƙa tayi kan Bellingham, Barcelona na zawarcin Leao

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na shirin tayi kan ɗan wasan Sunderland ɗan ƙasar Ingila, Jobe Bellingham, mai shekara 19. (Sun)

Chelsea da Barcelona sun nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Portugal Rafael Leao, mai shekara 25, daga AC Milan. (Calciomercato)

Manchester City na tattaunawa da wakilan ɗan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, a yayin da ta ke zawarcin ɗan wasan na Jamus mai shekara 21. (Football Insider)

Real Madrid da Bayern Munich su ma suna sha'awar ɗaukar Wirtz, wanda alamu ke nuna cewa zai iya barin Bayer Leverkusen a bazara. (Mundo Deportivo)

Arsenal da Liverpool da Chelsea na ci gaba da sanya ido kan ɗan wasan gaban Inter Milan da Faransa Marcus Thuram, mai shekara 27. (TBR Football)

Bayern Munich ta tattara bayanai game da Dean Huijsen na Bournemouth duk da cewa dan wasan bayan na Sifaniya mai shekara 19 bai kasance takamaiman ɗan wasan da ta ke hari ba a wannan bazarar. (Florian Plettenberg)

Ɗan wasan tsakiya na Jamus Joshua Kimmich, mai shekara 30, na shirin ya ƙulla sabuwar yarjejeniya da Bayern Munich har zuwa shekarar 2029. (Fabrizio Romano)

Juventus na son sake amincewa da wata yarjejeniyar aro kan Randal Kolo Muani a bazara wanda za ta ƙunshi zaɓin siyan ɗan wasan gaban na Faransa, mai shekara 26, daga Paris St-Germain. (Calciomercato)

Barcelona ta fara tattaunawa kan tsawaita kwantiragin golan Poland Wojciech Szczesny mai shekaru 34. (Nicolo Schira)

Tsohon daraktan wasanni na Atletico Madrid Andrea Berta ya amince da karɓar irin wannan matsayin a Arsenal, duk da sha'awar da manyan ƙungiyoyi kamar Manchester United da Paris St-Germain su ka nuna. (Sky Sports)

Everton za ta biya fam miliyan 40 don siyan ɗan wasan bayan Ecuador Joel Ordonez, mai shekara 20, daga Club Brugge a bazara. (Football Insider)

Manchester City na nazarin miƙa tayi kan ɗan wasan Crystal Palace ɗan ƙasar Ingila Adam Wharton, mai shekara 21. (TBR Football)

Ɗan wasan baya na Ingila Jarrad Branthwaite na iya zama ɗan wasan da yafi karɓar albashi mafi tsoka a Everton inda ɗan wasan mai shekaru 22 ke shirin miƙa buƙatar kwantiragin kusan fam 150,000 duk mako domin ya ci gaba da zama a ƙungiyar. (Football Insider)