Fulham ta miƙa tayin fam miliyan 20 kan McTominay

Asalin hoton, Getty Images
Fulham ta miƙawa Manchester United wani sabon tayin Fam miliyan 20 kan ɗan wasanta na tsakiya Scott McTominay.
Ana tunanin cewa United za ta yi watsi da tayin amma akwai rashin tabbas kan makomar ɗan wasan na Scotland bayan West Ham ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa a bazarar da ta gabata.
Da ya ke bayani a sanasanin horon wasannin share fage na United a Amurka, Koci Erik Ten Hag ya ce yana farin ciki da kasancewar McTominay a tawagarsa, amma bai tabbatar da cewa ɗan wasan mai sahekara 27 zai ci gaba da zama a kulob ɗin ba.
Ƙungiyar ta Old Trafford na ƙoƙarin samun kuɗaɗen da za ta yi cefanen ƴan wasa kuma yanzu da ɗan wasa mai tsaron baya Leny Yoro zai yi jinyar wata uku, ga kuma da ɗan wasan gaba Rasmus Hojlund shi ma yana fama da rauni, lamarin ya ƙara yi wa United ƙamari.
McTominay ya buga wasanni 32 a gasar Firimiyar bara, inda ya fara 14 a ciki daga benci, duk da dai ya buga wasan ƙarshe na cin kofin FA da United ta yi nasara kan Man City.







