Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Tanadin hukumomi kan rigakafin Maleriya 09/11/2024
Bayan shafe shekaru ana gwajin rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro a ƙasashen Ghana da Kenya da kuma Malawi, hukumar lafiya ta duniya ta amince da alluran rigakafin domin yaƙi da cutar.
Rigakafin farko da hukumar ta amince da shi, RTS,S/AS01 ya samu isa ga yara kusan miliyan biyu a waɗannan ƙasashe.
Yayin da rigakafin, R21/Matrix-M, shi ne na biyu da hukumar ta amince a yi amfani da shi.
Hukumomi a Najeriya, ƙasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar ta karɓi allurar miliyan ɗaya domin fara gwajinsu a jihar Kebbi da na Bayelsa.
ƙasashe tara na nahiyar Afrika, Benin, Burkina Faso, Burundi, Cameroon, jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, Liberia, Niger, Sierra Leone da Uganda sun sanya rigakafin cikin jerin rigakafin yau da kullum.
Amma ƙasashen Cape Verd da Masar sun samu shaidar kawar da cutar ta zazzabin cizon sauro daga WHO.
Kimanin mutane miliyan 233 ne suka kamu da cutar maleriya a shekarar 2022, wanda ya zo dai dai da kashi 94 cikin dari na masu cutar a duniya.
Haka kuma a nahiyar ne aka samu kashi 95 cikin dari na mutuwa sakamakon cutar a duniya, wato mutuwar kimanin mutane dubu dari 580 a wannan shekarar.
Yayin da yara ‘yan kasa da shekara biyar ne suka kasance kusan kashi 80 cikin dari na wadanda cutar ta kashe a nahiyar.
Ku latsa makunnin da ke sama domin jin tsare-tsaren da hukumomi a Najeriya suka ce suna yi kan fara amfani da allurar rigakafin na cutar maleriya.