Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Ko munshari na da illa a lokacin goyon ciki?
Yin munshari a lokacin bacci a tsakanin mata masu juna biyu abu ne da ya yawaita, a cewar masana.
Sai dai likitoci sun bayyana cewa yawan munshari a lokacin goyon ciki kan zama yana da alaƙa da wasu cututtuka, kamar hawan jini, cutar jijjiga da matsananciyar damuwa.
Amma hakan ba yana nufin duk mai cikin da ke munshari na fama da waɗannan larurori ba ne.
Ƙiba da yanayin kwanciyar mai juna biyu kan shafi hanyoyin iska, kuma hakan kan sanya ta yi munshari.
Yayin da kuma likitoci ke danganta munsharin wasu masu juna biyu da wata matsalar da ta shafi bacci, sleep apnea, lamarin da ke sanya numfashin mai bacci ya ɗauke, kuma a ƙware ko a samu sarƙewar numfashin bayan ya dawo.
Wasu daga cikin hanyoyin rage yawan munshari ga mai ciki sun haɗa da kwanciya ta gefe maimakon rigingine.
To domin jin ƙarin shawarwari da kuma sauran bayanai kan yawan munshari ga mai ciki, latsa makunnin da ke sama.