Ana ce-ce-kuce kan rataye wasu 'yan mata 'yan gida daya a Indiya

An wallafa

A farkon wannan watan, sa'o'i kadan bayan gano gawar 'yan uwa biyu rataye a saman bishiya a arewacin jihar Uttar Pradesh, 'yan sanda sun ce sun kawo karshen lamarin tare da kama mutane shida da ake zargi da kisansu.

Sai dai iyalan mamatan da wadanda ake zargi sun sanya ayar tambaya kan binciken, suna masu cewa bayanin da suka bayar ya sha bamban da wanda 'yan sanda ke fada. Ana kuma sukar cewa wasu 'yan siyasa da 'yan jarida da sun mayar da hankali kan addinin wadanda ake zargi.

Wakilan BBC Geeta Pandey da Vineet Khare sun ziyarci gundumar Lakhimpur, mai nisan kilomita 200 daga babban birnin yankin Lucknow, domin tattara bayanai kan ainahin abin da ya faru da ya dauki hankali a ciki da wajen kasar.

Bayanin 'yan sanda - kame da amsa laifi

Kasa da kwana guda da faruwar lamarin, 'yan sanda sun gudanar da taron manema labarai, inda suka bayyana kama mutanen, da wanda ya jagoranci lamarin dan kauyen Dalit mai makwabtaka, da wasu musulmai biyar da ke wani kauyen.

SP Sanjeev Suman ya ce mutanen sun amsa laifi tare da bayyana abin da ya faru.

Ya ce: ''Wanda ya jagoranci mummunan aikin ya gabatar da 'yan matan ga musulmai mazan biyu, daga nan suka zama abokai, kuma bisa radin kan su suka bi 'yan mazan a bayan babura".

"Wadanda ake zargin sun ce fusata ce ta sanya suka yi wa matan fyade tare da makure su har sai da suka mutu, saboda sun matsa musu da zancen aure. Daga nan sai suka kira maza biyu domin taimaka musu rataye 'yan matan a jikin bishiya.''

'Yan uwan wadanda ake zargin sun yi ikirarin 'yan sanda sun kama 'ya'yansu ba tare da hujja ba, an kuma ci zarafinsu lokacin ana tsare da su, duk da cewa yawanci kananan yara ne.

Me iyayen 'yan matan ke cewa

'Yan uwan matan sun dasa ayar tambaya kan labarin da 'yan sandan suka bayar cewa suna mu'amala da 'yan matan. Maza uku a kan babur ne suka sace 'yan uwan masu shekara 17 da 15, in ji mahaifiyarsu, wadda ita kadai ce ta ga abin da ya faru.

"Da na yi kokarin binsu da gudu, sai daya daga cikinsu ya min gula a ciki. Sai na fadi kasa," in ji mahaifiyarsu, tana zubar da hawaye lokacin hira da BBC. A lokacin da ta mike tuni sun yi gaba, ko kurarsu ba ka gani.

Gidan mai daki biyu a Dalit, wanda a baya ake yi wa lakabi da ''gagara badau'', ya na kusa da wara katuwar gonar rake, kuma babu wuya an nemi mutum an rasa saboda kararen raken da suka mamaye wurin.

Mahaifin 'yan matan ya ce ya na dawowa daga gona mahaifiyar yaran ta shaida ma sa mummunann labarin.

Nan da nan mutanen kauyen suka fita kungiya-kungiya domin neman 'yan matan cikin gonakin rake.

Bayan awa biyu da rabi, sun yi kicibis da gawar 'yan matan rataye a jikin bishiya su na reto, kuma babu nisa daga gidansu.

"Nan da nan mutane suka fara ihu, su na cewa 'ga su anan, ga su anan', in ji mahaifin ya na share hawaye, ''nan da nan muka sanar da 'yan sanda.''

Iyayen matan ba su amince da bayanin 'yan sanda da suka ce wai 'yan matan sun san wadanda ake zargin.

Labarin da suka ba da kan 'yan matan shi ne su na da kokari da hazaka, dukkn ayyukan gidan su ke yi, ba su da kwaramniya.

''Ba sa zuwa ko ina ba tare da dan rakiya ba,'' in ji dan uwansu. Mahaifinsu ya kara da cewa; ''Su na da saukin kai, 'yan sanda na shaci fadi ne kawai kan abin da ba su san yadda ya faru ba.''

Zargi - da harbin bindiga

Gidan musulmai biyar da aka zarga da aika-aikar ba shi da nisa da na 'yan matan.

Iyayensu sun ce ba su da masaniyar ko 'ya'yansu sun san 'yan matan, amma sun kafe 'ya'yansu ba su aikata kisa ba.

Daya daga iyayen mazan, da 'yan sanda sukai ikirarin an kama bayan an harbe shi a kafa lokacin da y yi yunkurin tserewa, ya yi ta faduwa ya na kuka a lokacin hira da BBC.

Ya ce da tsakar dare 'yan sanda suka kai farmaki gidanmu, tare da tambayar inda dan su ya ke, wanda ke hanyar dawowa daga wurin aiki a Hyderabad.

Dan na shi ya na sauka a tashar motar garin Oilibhit, aka cafke shi.

''Ina tare da 'yan sandan a cikin motarsu, amma sai suka sanya dana a wata motar ta daban. Amma 'yan sandan ba su ba ni damar ko yin magana da shi ba,'' in ji mahaifin kamar yadda ya zarga.

''Daga bisani na samu labarin an harbi da na a kafa. Ban san dalilin da ya sa aka harbe shi ba.

Amma 'yan sanda sun ce sun yi artabu kafin su cafke shi lokacin da ya ke niyyar tserewa.

Amma ba wani guduwa da ya so yi, ya fa dawo daga aiki ne. Don me ya sa zai gudu, alhalin bai yi laifi ba.''

"Idan an same shi da laifi, a rataye shi, amma kafin nan ku yi bincike sahihi mana,'' in ji Baban mutumin, ya kara da cewa ya na ganin binciken gwamnati ne kadai zai warware matsalar.

Sannan iyalan mazan sun ce karya 'yan sanda su ke yi da suka ce duka mazan manya ne, alhalin kanana ne.

Sun ce wani jami'in gwamnati da ya samar da ainahin katin shaidar yaran, daga daga ciki an haifeshi a shekarar 2008, hakan na nufin shekararsa 14, sai dayan mai shekara 17.

Mahaifiyar biyu daga ciki ta yi ikirarin 'ya'yanta ba su kai shekara 18 ba. Daya daga ciki ya nuna katin shaidar da ya nuna shekararsa 18, amma ta kafe shekarar dan ta 17.

Mista Suman, ya kuma yi watsi da ikirarin iyalan. ''Babu wata shaida da ta tabbatar da wadanda ake zargi yara ne.

Binciken jami'an lafiya ya tabbatar ba yara ba ne. Don haka indai ba wani bayani muka samu da ya yi karo da wanda aka samu ba, mu na musu kallon manya ba yara ba.''

Duk da cewa an yi ta jinjinawa ‘yan sandan, kan daukar matakin gaggawa na magance matsalar fyaden da ta faru a Lakhimpur amma duk da hakan an yi korafi kan wanda aka ambata da aikata laifin.

 

An kuma yi korafin an takurawa tsirarun Musulmi da ke jihar, zargin da jam’iyyar BJP ta musanta.

 

Mu koma batun fyaden baya-bayan nan

Ranar Laraba, mako guda da gano gawar ‘yan uwan biyu a rataye, ‘yan sanda suka tasa keyar mutane 4 da ake zargin tare da maida su kauyen na Tamoli Purva, domin bayanin ainahin abin da ya faru a cewarsu. Cikinsu har da wanda aka harba a kafa, ya na dingisa kafafu, na nade kafar da farar filasta.

 

Ya yin da suje tafiya zagaye da ‘yan sanda,  wani dan jarida ya ya cuna makarafo a kusa da bakinsu, tare d tambyar wadanda ake zargin, ko  ko sun yi danasanin abin da suka aikata.

 

"Ba mu san komai kan batun nan ba,ba mu da hannu a lamarin," in ji daya daga cikinsu.

 

Dayan kuma ya kada baki yace: "Ya ce baki day aba ma wurin da  aka aikata fyaden ba," in ji dayan.