Ra'ayi Riga: Ce-ce-ku-ce kan saya wa matar Tinubu motocin alfarma

Ra'ayi Riga: Ce-ce-ku-ce kan saya wa matar Tinubu motocin alfarma
An wallafa

Fadar shugaban Najeriya za ta kashe kusan naira biliyan 4.4 don saya wa matar shugaban ƙasa da fadar shugaban ƙasa motoci da kuma wata fiye da naira biliyan 13 don gyaran gidajen shugaban ƙasa da na mataimakinsa a Abuja da Legas.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke kukan matsin rayuwa da suke ciki, inda gwamnati take ƙara kiraye-kirayen jama'a su ƙara haƙuri.