Arsenal na zawarcin Nico Williams, AC Milan na son Guardiola a matsayin koci

Nico Williams

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nico Williams
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sabon daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta, a baya-bayan nan, ya gana da wakilin Nico William, ɗanwasan Athletic Bilbao domin tattaunawa kan ɗaukan ɗanwasan mai shekara 22 da ke buga wa Sifaniya. (Guardian)

AC Milan na duba yiwuwar ɗaukan kocin Manchester City Pep Guardiola da tsohon kocin Brighton Roberto de Zerbi, wanda a yanzu yake tare da Marseille. (Corriere della Sera - in Italian)

Liverpool da Chelsea na son ɗaukan ɗanwasan Bournemouth mai shekara 19 Dean Huijsen a wannan bazarar, amma za ta fuskanci gogayya daga Real Madrid ga ɗanwasan da aka yi wa farashin fam miliyan 50. (Independent)

Ɗanwasan gaban Masar, Mohamed Salah mai shekara 32 ya shirya tsaf domin tsawaita kantiraginsa a Liverpool bayan shafe watanni ana jita-jita. (Foot Mercato - in French)

Manchester United da Liverpool da Newcastle na zawarcin ɗanwasan Como mai shekara 19, Assane Diao. (Caught Offside)

Ɗanwasan Liverpool mai shekar 19 Ben Doak, wanda ke zaman aro a Middlesbrough, na iya komawa Everton a wannan bazarar kan yarjejeniyar fam miliyan 30. (Football Insider)

Arsenal da Liverpool da Nottingham Forest na nuna sha'awar sayen ɗanwasan Algeria Mohamed Amoura, mai shekara 24, wanda ke zaman aro yanzu haka a Wolfsburg daga Union St-Gilloise. (L'Equipe - in French)

Juventus na son ɗauko ɗanwasan Newcastle Sandro Tonali inda ƙungiyar ta Serie A ke kimanta darajar ɗanwasan mai shekara 24 a kan kusan fam miliyan 70. (Gazzetta - in Italian)

Newcastle za ta sabunta sha'awar neman ɗanwasan Crydstal Palace da Ingila Marc Guehi mai shekara 24 a bazara. (GiveMeSport)

Liverpool na tattaunawa da wakilan ɗanwasan Japan Takefusa Kubo, mai shekara 23, kuma suna iya ɗauko shi a bazara idan Real Sociedad ta gaza tsallakawa wasan Turai. (Teamtalk)

Aston Villa na fatan cimma matsaya da ɗanwasan tsakiyar Faransa Boubacar Kamara, 25, a sabon kwantiragi mai cike da tarihi shekara, domin kore duk wasu masu nuna sha'awar ɗaukansa a bazara. (Foot Mercato - in French)