Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Tare da alƙalan Hikayata 17/11/2024

Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Tare da alƙalan Hikayata 17/11/2024
An wallafa

A cikin shirin na wannan makon Usman Minjibir ya tattauna da alƙalan gasar Hikiyata ta 2024.

Alƙalan sun bayyana matakan da suka bi wajen tantance labaran da suka yi nasara a gasar ta bana.

A ranar 27 ga watan Nuwamban da muke ciki ne za a yi bikin karrama gwarazan da suka yi nasara a gasar a Abuja, inda za a ba su kyautar kuɗi lambobin yabo da takardun shaida