Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mourinho na son ya koma Newcastle, Brazil na matsi ga Guardiola
Pep Guardiola Manchester City na shirin sassauta matsayarsa kan zubin sabbin ƴanwasa a Janairu domin magance matsalar da yake fama da ita inda yanzu yake sa ido kan wasan baya na Atalanta da Brazil Ederson, mai shekara 25. (The I - subscription required)
Kocin Fenerbahce na Portugal Jose Mourinho, mai shekara 61, na sha'awar dawo wa gasar Premier kuma yana harin aikin Newcastle idan har Eddie Howe, mai shekara 46, ya bar St James' Park. (Guardian)
Hukumar ƙwallon Brazil na matsi ga kocin Manchester City Guardiola domin karɓar aikin horar da tawagar ƙasar. (The Athletic)
Newcastle na shirin ɗauko ɗanwasan gaba na Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, kan fam miliyan 50. (Football Insider)
Bayern Munich na son ɗauko ɗanwasan Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, wanda ke da damar ficewa kungiyar ta Lisbon club kan fam miliyan 60 (Sky Germany)
Barcelona na fatan doke Liverpool kan ɗanwasan Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 22, inda za ta hada da ɗanwasanta na gaba Ferran Torres, mai shekara 24 (Fichajes - in Spanish)
Bayern Munich ta sabunta kwangilar ɗanwasan baya Alphonso Davies, mai shekara 24, yayin da Barcelona da sauran manyan kungiyoyin Turai ke farautar ɗanwasan. (Bild - in German)
Tottenham na sa ido kan ɗanwasan Rayo Vallecano da Romania Andrei Ratiu, mai shekara 26, duk da ƙungiyar ta fi son tayi daga Real Madrid. (Fichajes - in Spanish)
Ana cike da kyakkyawar fata tsakanin ƴanwasan Manchester United saboda zuwa sabon koci Ruben Amorim. (Manchester Evening News)
Arsenal na tattaunawa kan sabuwar kwantaragi da ɗanwasan tsakiya mai shekara 17 Ethan Nwaneri (Teamtalk)
Ɗanwasan baya na Jamus Mats Hummels, mai shekara 35, na shirin barin Roma ya koma taka leda a Bundesliga a Janairu (Corriere dello Sport - in Italian)
Arsenal za ta jira har zuwa wata bazara kafin sayen ɗanwasan gaba maimakon Janairu. (Independent)
Ɗanwasan baya na Inter Milan Yann Bisseck, mai shekara 23, na shirin sanya hannu kan sabon kwantaragi wanda zai kawo karshen fatan West Ham na karɓo ɗanwasan na Jamus (Tuttosport - in Italian)
Hansi Flick ya farfaɗo da Barcelona ta hanyar bin matakai da suka haɗa da ɗa'a ta hanyar ajiye ɗanwasan da ya yi latti. (Marca - in Spanish)