Ra'ayi Riga: Zargin 'yan hamayya kan shari'o'in zaɓe a kotunan Najeriya

Ra'ayi Riga: Zargin 'yan hamayya kan shari'o'in zaɓe a kotunan Najeriya
An wallafa

A Najeriya jam'iyyun adawa na zargin gwamnati mai ci da amfani da karfin shari'a wurin murkushesu.

Wannan ya biyo bayan shari'o'in zaɓe da suka shafi jihohi, irinsu Zamfara da Kano da kuma Filato.

Mene ne ra'ayinku kan shari'o'in da kuma yada suka kasance? Ya kuma kuke kallon zargin da 'yan adawar ke yi?

Shin kuna ganin akwai bukatar gyara a bangaren shari'ar kasar? Wadannan da ma wasu na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirinmu na ra’ayi riga.