Kamaru ta gayyaci Onana bayan wata tara da ta dakar da shi

An wallafa

An sanar da sunan golan Manchester United Andre Onana a cikin tawagar 'yan wasan Kamaru da za su buga wasansu na karshe a neman shiga gasar cin kofin Afrika.

Sanarwar ta zo ne watanni tara bayan da hukumar kwallon kafar kasar ta dakatar da shi a tsakiyar gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.

Onana, mai shekaru 27, ya koma United ne daga Inter Milan a watan Yuli, wanda ya maye gurbin David De Gea a matsayin zabi na farko a Old Trafford, wanda ya bar kungiyar bayan shekaru 12.

Onana ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa wasa bayan da aka dakatar da shi saboda "dalilai na ladabtarwa", wanda ake tunanin ya samo asali ne daga rashin jituwa da kocin Kamaru Rigobert Song.

A wani abin da zai zama mai ban mamaki, tsohon dan wasan na Ajax zai iya buga wasan mai rabo ka dauka da Burundi a rukunin na uku ranar 12 ga watan Satumba, don naman gurbin shiga gasar wanda Ivory Coast za ta karbi bakunci a watan Janairu da Fabrairu shekara mai zuwa.

Namibiya ce ke kan gaba a rukunin da tazarar maki daya, amma ta kammala wasanninta da ya rage mata a rukunin, yayin da aka yi waje da Kenya daga wasannin.

Kamaru tana matsayi na biyu sakamakon kawallayen da ta ci, yayin da Burundi ke mataki na uku.