Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za mu horas da almajirai domin goga kafaɗa da sauran ƴan Najeriya'
Shugaban hukumar Kula da Almajirai da Yaran da ba sa zuwa Makaranta ta Najeriya, Dr Idris Idris Muhammad Sani ya ce nan ba da jimawa ba za su yaye almajirai 200 da za su goga da duk wani ɗan Najeriya a fannin Turanci ko Larabci ko kuma neman kowane irin aiki.
Ya ce tun lokacin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba shi jagorancin hukumar ya nemi da ya ta tabbatar da babu yaron da zai kasa cin abinci har sai ya yi bara.
"Hakan ne ya sa muka yi tsare-tsare da taruka wajen fito da hanyoyin da za mu cimma hakan.
Mun ɗauki almajira 200 ƴan ƙasa da shekara 16 a matsayin matakin gwaji sannan za mu sake ɗaukar wasu 200 na yaran da ba sa zuwa makaranta daga kudancin Najeriya.
Za mu ba su horo na watanni tara inda za mu koya musu Larabci da Turanci da sana'o'i domin samun damar rubuta jarrabawar kammala sakandare.
Wannan shaidar kammala sakandire za ta ba su damar ci gaba da karatu har jami'a ko kuma shiga aikin gwamnati kamar kowane ɗan Najeriya." In ji Dr Idris.
Dangane kuma da gina makarantu ga almajiran ƙasar, Dr Muhammad ya ce burinsu shi ne nan gaba su samar da makarantu 1000 ga almajirai domin su samu damar yin karatu kamar kowane ɗan Najeriya.