Matashiyar da ke bayar da hayar kayan biki a Kano

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Wata matashiya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bude shagon ba da hayar kayan biki da mata ke sanyawa a lokutan bukukuwansu.

Habiba Yusha'u, wacce aka fi sani da Beebas Glam, ta ce ta fara sana'ar ce bayan fahimtar yadda mata ke kashe kudi wajen sayen tufafi yayin bikinsu wadanda kuma ba su bukatar shi bayan biki.

"Idan aka yi lakari a kasar Hausa kusan duk bikin da za a yi, za ka ga amarya ta saka tufafi wanda sau daya kawai ake daura shi domin idan ta saka shi bayan biki za a rika mata kallon mahaukaciya".

Habiba tsohuwar mai sana'ar kwalliya ce amma a yanzu tafi mayar da hankali ne wajen ba da hayar kayan amare lokacin bikinsu.

Matashiyar ta ce akwai duk irin kayan da amarya ke bukata kuma cikin farashi mai sauki saboda ta fara sana'ar ce domin taimakawa talakawa da marayu tun da ita ma maraya ce.