Ra'ayi Riga kan janye zaɓen ƴar tinƙe a Najeriya

An wallafa

Cikin shirin na wannan makon, manyan baƙi sun tattauna ne kan batun janye zaɓen ƴar tinƙe da ƴan majalisar dokokin Najeriya suka yi.

Dama ƴan majalisar ne suka bijiro da batun kuma suka aika wa shugaba Muhammadu Bhari cikin ƙunshin sabuwar odokar zaɓen ƙasar da suka yi wa kwaskwarima, amma daga bisani shugaba Buhari ya ƙi sanya mata hannu saboda batun zaɓen ƴar tinƙen.

Ƴan majalisar sun ce sun amince su cire batun ƴar tinƙe ne don ba da damar amincewa da sauran ɓangarorin da dokar ta ƙunsa da suka shafi inganta zaɓukan ƙasar.