Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Gwamnatin Borno ke ƙarfafa wa iyaye gwiwar sa yara a makaranta
Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin yi wa yara ƙanana rajistar karatu, wani mataki da zai bai wa yara damar komawa makaranta.
Jihar ta Borno dai ta shafe shekaru tana fama da rikicin ƙungiyar Boko Haram da ya ɗaiɗaita yankuna da dama tare da haifar da koma baya a harkoki da dama ciki har da ilimi.
A wata ziyarar yini uku da gwamna Babagana Umara Zulum ya kai yankin Damasak - ɗaya daga cikin yankin da rikicin Boko Haram ya shafa, ya karfafa wa iyayen yara su amince su kai yaran nasu don yi musu rijistar shiga makaranta.
Alhaji Ali Kaka shi ne sakataren din-din-din na ma'aikatar ilimi ta jihar Borno ya ce wannan ba shi ne karon farko ba saboda a baya ma gwamnatin jihar ta taɓa ƙaddamar da shirin a Monguno.
Ya ce a shirin farko a ajin farko na makarantar firamare, an samu yara maza 439 sai yara mata 749.
A cewarsa, saboda rikicin Boko Haram, idan yara suka kammala ƙaramar sakandare, ba sa samun kai wa makarantun sakandare inda ya ce a wannan karo, za a buɗe makarantun sakandaren da ke Maiduguri, babban birnin jihar domin bai wa ɗaliban dama su koma azuzuwansu.
"Dama can wannan ɓangare, tun ma kafin abubuwan Boko Haram (akwai rashin damuwa daga wajen iyaye su kai yaransu makaranta), shi yasa a ka nanata cewa duk wanda ya kai yaransa makaranta nan gaba idan an kawo taimako, su za a taimakawa domin a ƙarfafa musu gwiwar kai yara makaranta" in ji Ali Kaka.
A yanzu dai ƙananan yara 'yan gudun hijira fiye da 1,100 ne aka sanya a makarantun firamare a garin na Damasak.
Rikicin Boko Haram da ya ɗaiɗaita yankin Arewa maso Gabashin Najeriya dai ya yi sanadiyyar raba yara da yawa da makaranta inda wasun su ke gararamba a kan tituna.