Bude makarantu a Kano: Yadda dalibai suka ji da matakin

An wallafa

Ranar Litinin 10 ga watan Agusta jihar Kano da ke Najeriya ta bi sahun wasu jihohi inda ta sake bude makarantu ga daliban da ke shirin rubuta jarrabawar WAEC.

Mun ji ra'ayoyin wasu daga cikinsu kan yadda suka ji game da sake bude makarantun bayan sun yi wata da watanni a rufe sakamakon cutar korona.