Adikon Zamani: Cin mutuncin mata a shafukan sada zumunta

An wallafa

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren shirin Adikon Zamani

Makwanni da suka wuce, masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu bayan da wata cikin masu amfani da shafukan ta ce a ganinta yin aure ba ci gaba bane.

Na so a ce mutane sun fito sun bayyana ra'ayoyinsa yadda ya dace, sabanin kalaman cin mutunci da zagi da aka rika aika mata.

Wannan lamari ya jefa ni cikin kogin tunani, kan yadda mata ke fuskantar wulakanci da cin mutunci a wadannan shafuka.

Sai nake ganin kamar babu girmamawa ko kamun kai idan aka zo batun mu'amala a shafukan sada zumunta.

Ko wane irin ra'ayi mace ta bayyana, sai an samu wanda zai zage ta ko ya wulakanta ta.

Wannan makon, mun zauna da babbar mai kula da shafin intanet na BBC Hausa, Halima Umar Saleh don tattaunawa a kan wannan matsalar.